
Reverend Ezekiel Dachomo daga Jihar Filato ya tsinewa Reno Omokri saboda yace babu wata Mhuzghunawa ko Khisan Kyiyashi da akewa Kiristoci a Najeriya.
Ezekiel wanda shine shugaban cocin Church of Christ in Nations (COCIN) a karamar hukumar Barkin Ladi yace Reno Omokri yana hada kai da Gwamnati yana cimma wani burinshi inda yace amma abin ya zo karshe a wannan karin ba zai yi nasara ba.
Hakana Ezekiel ya kuma tsinewa wasu membobin CAN da suma suka ce ba’awa Kiristoci Kyisan Kyiyashi a Najeriya
Yace abinda kawai zai tseratar da Reno Omokri shine idan ya tuba.
Lamarin ya jawo muhawara me zafi a kafafen sadarwa inda wasu suka rika kiran Reno Omokri ya roki faston yafiya.