
Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin Ya bayyana yanda ya koma gida ya tarar da matarsa ta kulle masa gida ta tafi Kano.
Yace tana can tana cewa, wai Allah ya bata miji na gari to menene na kulle mai gida?
Ya bayyana cewa, Tana ta cewa wai ta auri dan Bariki, yace kusan shekara guda kenan da suka yi aure amma bai taba kwana a waje ba.
Gfresh ya bayyana cewa, Kada ta sake dawowa gidansa.