
Wani sabon Bidiyon ‘yan kwallon Najeriya, Super Eagles ya bayyana inda aka ji suna tattauna cewa ba’a biyasu hakkokinsu ba.
An dauki Bidiyon ne kamin wasansu da Morocco wanda Moroccon ta fitar dasu a wasan Penalty.
Lamarin dai ya jawo cece-kuce sosai inda ake dorawa hukumar NFF alhakin hakan.