
Me baiwa Gwamnan Kano shawara akan harkokin kafafen sada zumunta, Salisu Yahaya Hotoro ya yi wani Rubutu da ake zargin da Kwankwaso yake, duk da bai kira suna ba.
Ya rubuta cewa, Kwanannan mutane zasu fahimci wanene ya ci amanar mutanen Kano kuma wanene ya tsaya tare dasu yake kare muradinsu.
Yace dambarwa irin ta Novemed, data Scholarship, da dambarwar sayar da filaye, dambarwar tsaftace ruwan Kano, da sauran rikita-rikitar cin hanci da Rashawa sune suka kawo mu matsayin da ake yanzu.
Kamar yanda Imran U. Wakili ya ruwaito(@IU_Wakilii)