
Rahotanni sun bayyana cewa, Farashin man fetur ka iya kai Naira 1000 kowace lita.
Hakan na zuwane bayan da farashin danyen man fetur ya tashi a kasuwar Duniya.
‘yan kasuwar man sun shaidawa majiyar Hutudole cewa, farashin ka iya tashi nan da kwanaki masu zuwa. A ranar Alhamis ne dai farashin na danyen man fetur ya tashi zuwa dala $70 akan kowace ganga a kasuwar Duniya.
Dangote na sayar da man fetur dinsa akan farashin 739 zuwa 839 akan kowace lita a yanzu.