
Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon shugaban hukumar gyaran Fansho ta kasa, Abdulrashid Maina ya yanke jiki ya fadi.
Me magana da yawunsa ne ya bayyana hakan inda yace, Maina ya fadine yayin da yake kan matattaqalar hawa Ofishinsa.
Yace da ya fadi, Kansa ya bugu a kasa inda tuni aka garzaya dashi asibiti.