Wednesday, January 15
Shadow

Maganin kurajen fuska

Akwai hanyoyi da yawa da ake magance matsalar kurajen fuska. A cikin wannan rubutu, zamu yi bayani kan yanda ake magance kurajen fuska ta hanyoyi daban-daban.


Saidai kamin mu fara, a sani cewa, idan ana da kurajen fuska, kada a rika wasa dasu da hannu ko sosawa, ko da suna kaikai kuwa. Hakan zai kara dagula matsalar ne maimakon ya magance ta, kai cuta ma zata iya shiga, dan haka a kiyaye.

Hanyoyin da za’a iya amfani dasu a matsayin maganin kurajen fuska sun hada da:

Ana Amfani da kankara ko ruwan Sanyi: Idan aka dora kankara ko ruwan sanyi akan kurajen fuska, suna daina kaikayi da kumburi kusan nan take.

Karanta Wannan  Gyaran fuska da tumatir

Ana iya samun kankarar a nade a tsumma me tsafta a rika dorawa a jikin kurajen, ko kuma a samu ledar ruwa me sanyi a rika dorawa.

Idan an dora a rika barinshi yana kai mintuna 10 akalla.

A maimaita har iya yawan da ake so.

Idan kuma akwai kurajen a wasu bangarori na jiki da zasu yin wahalar kaiwa da hannu, sai a yi amfani da ruwan sanyi a yi wanka, duk ya wadatar.

Hanya ta gaba itace ta amfani da Aloe Vera:

Shekaru aru-aru da suka gabata an rika amfani da Aloe Vera wajan maganin ciwo da kumburi da sauran matsalolin fata.

Za’a iya siyo ruwan Aloe vera wanda ba’a hadashi da komai ba, ko kuma idan akwai Aloe vera a gida a tsinko ganyen a fere koren ganyen da ya lullubeshi a matse ruwan a rika shafawa akan kurajen, idan an ga reaction a dakata a tuntubi likita. Mun yi rubutu akan yanda ake amfani da Aloe Vera wajan gyaran fuska.

Karanta Wannan  Amfanin ridi a fuska

Hanya ta gaba ta Maganin kurajen fuska itace ta amfani da Man Kwakwa:

Man kwakwa na da matukar amfani kwarai wajan warkewar ciwo da maganin tsufa da sauransu.

A samu man kwakwa me kyau wanda babu gauraye a rika shafawa akan kurajen fuska a hankali na tsawon kwanaki, insha Allahu za’a samu waraka.

Idan an shafa an ga Reaction, kada a ci gaba da amfani dashi,a tuntubi likita.

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *