Thursday, February 5
Shadow

Da Duminsa: Ji Wata magana da Kwankwaso yayi da zata jawo a kamashi a Bincikeshi

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar lauyoyin Najeriya, NBA sun ce zasu aikawa da hukumar ‘yansandan Najeriya da sauran jami’an tsaro korafi dan a biciki tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kan wani ikirari da yayi.

Kungiyar ta bayyana hakane bayan zaman kwamitin zartarwasta, watau NEC

Sakataren kungiyar ta NBA, Etaba Agbor ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Maganar da ake zargin Kwankwaso da yi shine, yace a shakerar 2019 ya dauki Abba Kabir Yusuf zuwa ganin alkalan kotun koli ta Najeriya bayan da hukumar zabe me zaman kanta, INEC ta bayyana zaben Kano a matsayin Inconclusive, watau wanda bai kammalu ba.

Karanta Wannan  YANZU-YANZU: An daura auren fitaccen mawaki Dauda Kahutu Rarara da babbar hadimarsa Aisha Humaira a birnin Maiduguri na jihar Borno. Wane fata kuke masu?

A karshe dai kotun kolin ta tabbatarwa da Gwanduje a wancan lokacin cewa shine yaci zaben.

Wannan magana ta tayar da hankuka musamman tsakanin Lauyoyin Najeriya inda suka ce hakan kamar batawa alkalai sunane da nuna cewa an sasu sun aikata abinda ba bisa doka ba.

Lauyoyin sukace wannan abin zai iya sa ‘yan Najeriya su daina ganin Alkalai ko kotu da daraja a rika tunanin wasu manyan mutane na juyasu.

Dan haka ne kungiyarsu ta Lauyoyin suka yanke shawarar mikawa hukumar ‘yansanda da sauran jami’an tsaro korafi a hukumance dan a binciki wadannan kalamai na Kwankwaso.

Idan ba gaskiya bane a karyatasu, idan kuma gasiyane a hukuntashi da sauran wadanda ke da hannu a lamarin.

Karanta Wannan  Likitoci sun mana kadan matuka duk sun tsere kasashen waje>>Jihar Kwara ta koka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *