
Rahotanni daga Thecable sun bayyana cewa, Kasar Amurka ta bukaci a bata matsuguni a Najeriya inda zasu ajiye tashar man jiragensu.
Tashar zata rika baiwa jiragensu marasa matuka taimako a aikin kawar da matsalar tsaro a Najeriya.
Rahoton yace an bayyana wata jiha ta Arewa a matsayin jihar da zata baiwa Amurkar matsugunin.