Sunday, February 8
Shadow

Kalli Bidiyon: Muna ciyar da Masu laifi Akan Naira 780 kowace rana, hakanan muna ciyar da karnukan aiki akan Naira 800 a kowace rana>>Inji Hukumar gidan gyaran hali ta Najeriya

Hukumar gidan gyaran hali ta Najeriya, Nigerian Prison Service tace tana ciyar da kowane me laifi akan Naira 780 a kowace rana.

Sannan tana ciyar da karnuka akan Naira 800 a kowace rana.

Shugaban hukumar ne ya bayana haka yayin da yake gabatar da kasafin kudin hukumar na shekara a gaban majalisar tarayya.

Sanata Adams Oshiomhole wanda shine ya jagoranci zaman ya kalubalanci cewa, ta yaya za’a rika ciyar da karnuka fiye da mutane?

Karanta Wannan  Yarbawane suka fi kowace kabila a kasarnan yin gwajin DNA dan gano cewa ko matansu sun ci amanarsu ta hanyar basu 'ya'yan da ba nasu ba, Hausawa basu cika yin wannan gwaji ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *