
Wata ‘yar Bariki da suka shiga dakin Otal ita da wani a Abuja ta tafka masa mummunar sata.
Sin shiga Otal dinne ranar Alhamis, inda rahotanni sukace mutumin be ankara ba sai tashi yayi yaga babu wayarsa da mota da Laptop.
Cikin gaggawa ya sanar da masu kula da Otal din inda aka sanar da ‘yansanda.
Kakakin ‘yansandan Abuja, SP Josephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace suna kan bincike.