
Gwamnatin tarayya ta bayyanawa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai cewa, bai fi karfin doka ba.
Hakan ya fito ne daga bakin me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ta shafinsa na X inda yake martani kan kalaman El-Rufai na cewa, yana sauraren wayar da me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu ke yi.
ElRufai ya bayyana hakanne a hirar da aka yi dashi a Arise TV inda ya zargi Malam Nuhu Ribadu da bayar da umarnin a kamashi ta hanyar kiran waya ya bayar da umarni.
ElRufai ya bugi kirjin cewa, suma suna sauraron hirarrakin wayar gwamnati.
Onanuga yace hakan ba karamin laifi bane kuma ya kamata a binciki El-Rufai da ‘yan koronsa, idan wannan ikirari nasa ya zama gaskiya a hukuntashi.