Friday, June 26
Shadow

Da Duminsa: Sojojin kasar Amurka sun shigo Arewa, an bayyana jihar da suka sauka

Rahotanni sun bayyana cewq sojojin Amurka sun shigo Arewa.

Sojojin dai kwararru ne wanda zasu baiwa sojojin Najeriya horo akan dabarun Yaqi.

Rahotanni sun ce sojojin sun kai su 200 kuma sun saukane a jihar Borno.

Duka hukumomin Najeriya dana kasar Amurka aun tabbatar da wannan labarin.

Rahoton yace jirgin sojojin Amurka ya sauka a Maiduguri da daren ranar Alhamis, hakanan ranar Juma’a an kuma ga wasu jiragen guda 3 suna sauke kaya a Maiduguri.

Zuwa yanzu dai sojojin Amurkar 100 ne suka iso Najeriya inda ake tsammanin sauran zasu zo nan gaba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: An min Alfarma na shiga inda Qabarin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) yake>>Inji Tauraron fina-finan Hausa, Ibrahim Shahrukhan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *