
Wani Bidiyo Tauraron mawakin, Dauda Kahutu Rarara yana gaisawa da gwamnonin jihohin Borno da Gombe ya dauki hankula.
Da yawa sun bayyana cewa, Rarara ya mayar da gwamnonin Abokansa.
Saidai yayin da Gwamna Zulum da Inuwa Yahya suka gaisa da Rarara, Gwamnan jihar Adamawa, Ahmad Fintiri ya ki gaisawa da Rararan inda ya wuce abinsa.