Saturday, June 27
Shadow

‘Yan jihar Kogi sun fito sun nuna rashin jin dadinsu kan yanda Gwamnan Kaduna Malam Uba Sani ya ture Gwamnansu Usman Ododo a wajan taron ganawa da manema labarai

Wasu ‘yan jihar Kogi sun fito sun nuna rashin jin dadinsu kan yanda gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani ya ture gwamnan jiharsu, Usman Ododo.

A Bidiyon wanda ya rika yawo a kafafen sada zumunta, wanda kuma hutudole a kawo muku, An ga Gwamna Ododo na tsaye kusa da Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma kamin Gwamna Malam Uba Sani ya tureshi.

Mutanen na jihar Kogi da suke da kungiya a shafinsa X sun bayyana hakan da rashin girmamawa inda suka ce dolene Malam Uba Sani ya fito ya baiwa gwamnan su hakuri.

Sun ce wannan abu ya zamarwa gwamnansu abin kunya ana maganarsa ana masa dariya.

Karanta Wannan  Subhanallahi: Wannan wani fasto ne da yayi ikirarin wai sun yo chat ta WhatsApp shi da Allah

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *