Friday, June 26
Shadow

Matar Tsohon Gwamnan Kaduna, Hajiya Hadiza Ismail El-Rufai ta bayyana kayan aikinta da ICPC suka dauka da suka je bincike gidan mijinta wanda a tunaninsu shine na’urar yiwa waya kutse

Matar tsohon Gwamnan Kaduna, Hajiya Hadiza Ismail El-Rufai ta wallafa a shafinta cewa, ICPC sun dauke mata na’urar da take amfani da ita a banki.

Tace tana rantsuwa da Allah na’urar ba ta kutsen waya bace.

Ta bayyana cewa, cikin kayan da ICPC suka bayyana cewa sun dauka daga gidan Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, sun manta su bayyana wannan na’urar tata.

ICPC dai sun bayyana wayoyi da kwamfutocin tafi da gidanka a matsayin abubuwan da suka gano a gidan malam Nasiru Ahmad El-Rufai.

Karanta Wannan  Wata mata wadda tace ita 'yar Kwangila ce, tace ta kaiwa Ministan Ayyuka, David Umahi kayan aiki na Naira Miliyan 304 Shekaru 12 da suka gabata amma yaki biyanta

A baya kuma sun zargi cewa, sun gani na’urar yiwa waya kutse.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *