Saturday, May 2
Shadow

Kalli Bidiyon: An dakatar da malamin makaranta a jihar Kebbi Saboda yace baya son Tallafin shikafar da Gwamnati ta bayar

Rahotanni daga jihar Kebbi na cewa, an dakatar da wani malamin makaranta a jihar saboda ya fito ya soki rabon shinkafa da masa Sa’i guda da aka bashi.

Malamin a wani Bidiyonsa da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta an ganshi yana fadar cewa shi bai gode ba a matsayinsa na malamin makaranta da aka bashi wannan a matsayin tallafi.

@jalalkmb

A MATSAYINA NA MALAMIN MAKARANTA WANNNA SHINE RABON DA MAI GIRMA GWAMNA DR NASIR IDRIS KAURAN GWANDU YA BANI DA SUNAN TALLAFI HMMMMMMM.HAHAHAHAHA.UBANGIJI

♬ original sound – Abduljalal Usman Kamba

Sahara Reporters ta wallafa cewa, an dakatar da malamin saboda wannan Bidiyon.

A wata takardar dakatarwar da Sahara Reporters ta wallafa, anga cewa an dakatar da malmin me suna Abduljalal Usman na tsawon watanni 3 ba tare da Albashi ba.

Karanta Wannan  Bayan da Hadiza Gabon tasa aka kamashi, Rahama Sadau ta sa an sako Zaharaddeen Sani daga wajan 'yansanda

Takardar dai ta zargeshi da sakaci da aiki.

Amma a zahirin gaskiya da yawa sun ce saboda wancan Bidiyon ne da yayi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *