
Malam Abdulrahman Umar Sautussunnah ya bayyanawa mata cewa idan ba su shirya yiwa mijinsu wanki da guga ba to basu shirya yin zaman aure ba.
Malam ya bayyana hakane a wajan wani karatunsa inda yace ba wai yana gayawa maza su rika saka matansu wanki da guga bane, yana gayawa mata irin nauyin hakkin mazajensu dake kansu.