Tuesday, March 24
Shadow

EFCC sun kulle gidaje da kasuwancin Tsohon Ministan shari’a Abubakar Malami

A ranar Litinin, EFCC sun kulle gidaje da kasuwancin tsohon Ministan shari’a Abubakar Malami.

Rahotanni sun bayyana cewa EFCC sun rubuta da jan fenti cewa an kulle gidajen kada wanda ya shiga.

A wani Bidiyo da ya watsu a kafafen sada zumunta, An ga Malami yana tambayar EFCC din ina umarnin kotu da yace a kulle masa gida?

Malami dai yace umarnin farko da kotu ta bayar ya dina aiki.

Saidai jami’an EFCC din sun bashi amsar cewa zasu iya kulle gidajen nasa tunda har yanzu ana kan binciken su.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Bazan iya barin waka in koma makaranta ba saboda, masu digiri da yawa basu da abinda nake dashi irin su waya, mota>>Inji Bilal Villa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *