
Tauraron fina-finan Hausa, Sadiq Sani Sadiq yayi kira ga ‘yan Arewa kada su sake zaben gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu saboda azzaluma ce.
Sadiq ya bayyana hakane a wani Bidiyonsa daya dauka a wata kasuwa inda aka ga yana magana cikin fushu.
Ya zargi gwamnatin Tinubu cewa bata son Arewa, inda yace sun kawo haraji da Rashin Tsaro.
Ya karkare maganarsa da cewa kada a sake zaben Tinubu a matsayin shugaban kasa inda yace idan kunne yaji….