
Biyo bayan rade-radin da ake ta yayatawa cewa Babban Malamin Addinin Islama dake tsare a hannun Hukumomin Najeriya, Sheikh Khalifa Sani Zaria ya rasu.
Rahotanni daga PRNigeria sun tabbatar da cewa malam yana nan da ransa bai rasu ba.
Wata majiya daga Hukumar ta DSS ce ta bayyanawa PRNigeria hakan inda tace malam nanan Hukumomin soji dana DSS na masa tambayoyi.
Ana zargin Malam da karbar Naira Miliyan 2 ne dan yiwa sojan dake shirin yiwa shugaba Tinubu juyin Mulki Addu’a, saidai iyalan malam sun karyata wannan zargi.