Saturday, June 27
Shadow

Ta bayyana a fili cewa, Gwamnatin Tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne ta dauki nauyin Fulanin da suka takura ma yankinmu a Mulkinsa>>Inji Kungiyar Kare muradun Inyamurai ta Ohanaeze Indigbo

Kungiyar kare muradun Inyamurai ta Ohanaeze Indigbo ta bayyana cewa Gwamnatin tsohon shugaba kasa, Muhammadu Buhari ce ta dauki nauyin fulanin da suka rika damun yankinsu da hare-haren.

Kungiyar tace tun bayan da shugaba Buhari ya sauka a mulki sannan ya bar Duniya Fulani suka daina kai musu hare-haren da suke kai musu.

Mataimakin shugaban kungiyar, Mazi Okechukwu Isiguzoro da me magana da yawun kungiyar, Chief Thompson Ohia ne suka bayyana hakan.

Sun bayyana cewa, Rikicin ya lakume rayukan mutane 2,960 a yankin nasu.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: A wannan karin ma Tauraruwar fina-finan Hausa, A'isha Najamu ta sake yin Bikin Ashura, inda mutane suka cika da mamaki suna cewa da gaske 'yar Shi'a ce

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *