
Bidiyon wasu kalamai na gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda sun dauki hankula a kafafen sada zumunta inda aka ji yna cewa:
Mutane idan an musu Alheri, an musu aiki sun sani, idan ba’a musu ba sun sani, ba zamu hana mutane su yanke hukunci kan abinda suke so ba, idan an musu Alheri su mayar da Alheri.
Wasu dai sun fassara wadannan kalamai da cewa, kamar hannunka mai sandane ga talakawa kada su zabi Gwamnatin Bola Ahmad Tinubu.