
Me magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa, sun yi yunkurin yiwa Nafiu Bala Gombe ihisani dan ya hakura kada ya kawo musu matsala a jam’iyyar ADC amma abu ya faskara.
Ya bayyana cewa dalili kuwa shine ba kananan kudade da motoci da gida da jami’an tsaro Gwamnati ta bashi ba.
Yace kuma da Nafiu Bala Gombe ke cewa wai bai sauka daga shugabancin ADC ba karya yake.
Yace takardar da yake karyatawa yake cewa wai kwaikwayar sa hannunsa aka yi, karya yake, shine ya rubutata da kansa, sannan idan da gaske kwaikwayar sa hannunsa aka yi, me yasa bai kai korafi wajan hukuma ba dan kuwa kwaikwayar sa hannun mutum ai babban laifine.
Nafiu Abdullahi dai ya maka su Atiku a kotu inda yake zargin sun masa karfa-karfa sun kwace masa shugabancin jam’iyyar ADC.