
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayar da labarin yanda aka shirya munafurcin tsigeshi a matsayin Gwamna tare da hadin gwiwar mataimakinsa da ya sauka, Gwarzo.
Gwamnan yace an shirya tsigeshi ne sai kuma Gwarzo ya maye gurbinsa.
Yace amma sai Allah bai basu nasara ba.
Gwamnan ya bayyana hakane a yayin ganawa da wasu magoya bayansa.
Yace yaji ance mataimakin nasa ya sauka daga mukaminsa amma har yanzu shi bai ga takardar ajiye aikin nasa ba.