Monday, April 13
Shadow

Kalli Bidiyon: Ta Fadan Cacar baki ya barke tsakanin Atiku Abubakar da Kashim Shettima

Fadan cacar baki ya barke tsakanin tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.

Kashim Shettima ne ya fara tsokana inda yace Atiku ya fadi ayyuka 8 na ci gaba da yayi a Arewa da mutane 8 da ya taimaka a Arewa.

Saidai a martaninsa, Atiku yace wannan rashin kunyane, Kashim Shettima bashi da kunya, domin a girme, ya girmeshi bai kamata ya kalleshi ya rika gaya masa irin wannan maganar ba.

Sannan yace ba zai bashi amsa ba.

Atiku yace idan ma aikin Gwamnati ne, yafi Kashim Shettima iyawa da Kwarewa.

Karanta Wannan  Wani bawan Allah ya rasu ana tsaka da Sallar Asuba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *