Friday, June 26
Shadow

Matsalar tsaron Arewa ta kai matsayin Yaqi>>inji Kungiyar Tuntuba ta Arewa

Kungiyar tuntuba ta Arewa, ACF ta bayyana cewa, matsalar tsaron da ake fama da ita ta kai matsayin yaki.

Kungiyar tace tana kira ga Gwamnati data karkatar ta hankalinta da ma dukkan wani abu daya shafi kudi dan ganin an magance wannan matsala.

Kungiyar ta bayyana matsayar tane bayan zaman data yi.

Zaman ya samu halartar Tsohon shugaban sojoji, Janar Tukur Yusuf, Da Tsohon shugaban ‘yansanda, Muhammad Abubakar, da tsohon sakataren majalisar Dinkin Duniya, Tijjani Muhammad-Bande, da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Mahmud Ahmad, da shugaban kungiyar, Bashir Dalhatu.

Sun bayyana cewa matsalar tsaron na jefa musamman yankin Arewa cikin tawayar tattalin arziki da kuma daidaita iyalai da sauransu.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo:Jama'ar Katsina ku yi Hakuri, kamin in hau mulki na yi Alkawarin duk wata zan rika bada bayanin yawan kudaden da muka samu da yawan wanda muka kashe, amma yanzu da na zama Gwamnan naga abin ba zai yiyu ba>>Inji Gwamnan Jihar Katsina Dikko Radda

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *