Wednesday, April 22
Shadow

Da Duminsa: Dangote zai fara yin Omo da Sabulun wanki da kuma Robobi

Rahotanni sun bayyana cewa, Attajirin Najeriya Aliko Dangote zai fara yin Robobi da Omo da sabulun wanki.

Dangote zai fara hakanne a matatar man fetur dinsa dake Lekki Lagos inda ya hada kai da kamfanin Honeywell.

Matatar ta Dangote tana samar da sinadaran samar da sabulu da omon wanki da kuma robobi.

Hakanan ba a Najeriya kadai zai rika sayar dasu ba hadda kasashen Duniya

Wannan sabon kamfani nasa rahotanni sun ce idan ya tabbata zai zama mafi girma irinsa a fadin Duniya.

Karanta Wannan  Malamin Jami'a ya rigamu gidan gasiya bayan da ya shiga dakin Otal da dalibarsa 'yar aji 2

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *