
Wani me hada mata da maza masu neman aure ya koka da wata da ya hadata da wani mutum.
Yace ya hadata da mutumin ne inda a ranar farko da suka fita taci abincin Naira 200,000.
Yace a rana ta biyu da suka fita ta kawo abokanta 4 inda suka ci abincin Naira 1,053,000.
Saurayin yace zai biya kaso 70 cikin 100 na kudin su kuma su biya sauran amma suka kiya.
Daga baya dai saurayin ya tafi ya barsu sai da aka rike motar daya daga cikinsu a gidan abincin.