
Wannan wani barawo ne da aka kama ya shiga wani Kango da ake gini ya sace bokitan fenti guda 60 wanda darajarsu ta kai Naira Miliyan 1.5.
Ya tsiyaye fentin a kwata ya rika sayar da bokitan akan Naira 1000 kowanne inda ya tashi da Naira 60,000.
Lamarin ya baiwa mutane mamaki sosai.