
Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ya bayyana cewa ya daina shan giyane saboda kunya duk da yasan cewa yasan giyar halas ce.
Yace dalilin da yasa yake shan giya shine ya gani a baibul cewa Jesus ya mayar da ruwa giya.
Yace dalilin da yasa ya daina sha shine, wata rana ya je yayi wa’azi a sansanin majalisar Dinkin Duniya dake Somalia ya kammala sai ya tafi wani gidan cin abinci dan ya sayi giya.
Yace yana shiga sai ya tarar da mutane na ta shan giya amma suna ganinsa sai suka boye giyar, yace sai ya matsa kusa da wani yake tambayarsa me yasa suka boye giyar da suke sha?
Sai yace ai shi malam ne basa son yaga suna shan giya.
Yace daga nan yawa kansa fada yace duk da giyar ba halas bace amma ya daina sha.