Wednesday, April 29
Shadow

Jam’iyyar ADC ta bayyana matakin da zata dauka bayan da Kotu tace kada INEC ta yadda da sabbin shuwagabannin ta

Jam’iyyar ADC reshen su David Mark, Atiku, Kwankwaso da sauransu, sun bayyana matakin da zasu dauka bayan da kotu tace kada INEC ta yadda da zaben da suka gudanar na zabar shuwagabannin su.

A sanarwar daya fitar me magana da yawun jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa, zaben shuwagabannin da suka yi be soke shuwagabancin jam’iyyar a matakin jihohi ba.

Inda suka ce shuwagabannin jihohi na jam’iyyar zasu ci gaba da shugaban cinsu har su kammala.

Saidai Bolaji Abdullahi yace sun samu hukuncin kotun kuma zasu nemi lauyoyinsu su basu shawara kan abinda ya dace su yi.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon wasu na rokon Kabarin Shehu ya kawowa Najeriya saukin tsadar man fetur ya dauki hankula

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *