
Wani matashin Bayerabe ya bayar da labarin yanda ya dirkawa Budurwarsa da suka hadu a jami’a ciki.
Yace tun suna ajin farko a jami’a suka fara soyayya a shekarar data gabata, kuma takan je gidansa ta kwana.
Kwatsam sai ta gaya masa cewa ta dauki ciki.
Yace yayi farin ciki amma ita bata yi ba saboda tana tunanin iyayenta ba zasu yaddaba.
Yace ya bata shawarar ta zauna a gidansa har sai ta haihu sai su jewa iyayenta da dan da suka haifa, inda ta amince.
Saidai iyayenta sun samu labarin inda suke zaune inda mahaifinta ya je ya dauketa.
Yace shi kuma yana sonta tunda mahaifinta ya dauketa ya kasa samun nutsuwa.
Shine ya je ya samu iyayensa aka je aka baiwa iyayenta hakuri suka hakura, yanzu an ce ya bari idan ta haihu za’a daura musu aure.