
CIKAKKEN BAYANI
Matashi da ya tarwatsa rayuwar yarinyar nan sunansa Muhammad Hassan (Bossman) lambar wayansa 08185**7448 dan jihar Kano ne, ban fitar da cikakken nambar wayansa ba da kuma anguwar da yake a Kano saboda dalilai na bincike
Ita kuma yarinyar a jihar Kaduna take, ba zan fadi cikakken sunanta da anguwarsa ba saboda kiyaye mutuncinta da kuma anguwarsu
Bossman ya hadu da yarinyar ta sanadin media, ya fara nemanta da sunan soyayya, ya yaudareta da cewa zai aureta, ya bita Kaduna ya kama Hotel ya fara rabata da budurcinta
Shine mutum na farko da ya fara zina da ita, wannan bidiyo na tsiraci dake yaduwa ya kai shekara guda da yinsa, bayan ya gama |a|ata rayuwar yarinyar sai yace gaskiya shi ba zai iya aurenta ba
Shikenan ta watsar da shi, ta samu wani zai aureta, da wannan tsinannen da ake kira Bossman yaji labarin zata auri wani, sai ya fara aika mata wannan bidiyo na barazana ta hannun kawarta, cewa idan ta kuskura tace zata auri wani zai watsa bidiyon
A haka dai har wanda ta samu daga baya zata aura ya samu labari, kuma yace ya amince zai aureta a haka matukar bidiyon bai fita ba
Ana haka yanzu saura wata daya a daura mata aure, to da wancan tsinannen yaji labari sai ya saki bidiyon a media don ya hanata aure ya kuma tarwatsa mata rayuwa
Masu ganin laifin yarinyar ku san irin kalaman da zaku fadi kafin Allah Ya jarrabeku, domin ‘ya’yanku da kuka haifa da kannenku mata basu fi karfin tsinannun maza su yaudaresu su bata musu rayuwarsu ba
Muna kan tattaunawa da iyayenta don daukar matakin shari’a akan tsinanne Bossman, sai ya girbi sakamakon abinda ya aikata da taimakon Allah

ABIN TAUSAYI
Chatting da yarinyar nan tayi da kawar mahaifiyarta bayan bidiyon lalatar da wani tsinanne yayi da ita ya bayyana a media akwai alamun fargaba cikin kalamanta
Wannan magana da tayi yana mai kama da wanda yake shirin kashe kansa, na samo inda yarinyar take, na samu tsinannen da ya mata zaluncin nan
Na isar da shawara da nasiha zuwa ga iyayen yarinyar, na farko su kwantar da hankalinsu akan wannan jarrabawa, na biyu su sa ido sosai a kan yarinyar domin wannan chat din da tayi ya nuna alamun zata iya aikata suicide
Saurayinta ne, cin amanarta yayi, zuwa jimawa zan baku cikakken bayanin abinda ya faru da matakin da za’a dauka Insha Allah