Friday, June 26
Shadow

Kalli Bidiyon: Idan ina son kudi, kawai zan daga wayane in Kira shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu >>Inji Babachir David Lawal

Tsohon sakataren Gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal ya bayyana cewa ba siyasar kudi yake yi ba.

Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channels TV inda yace ba gaskiya bane cewar da ake wai Hayatu-Deen ya bashi kudi dan ya taimaka masa ya ci zaben fidda gwani na dan takarar jam’iyyar ADC.

Yace Hayatu-Deen bashi da kudin da zai bashi a yanzu.

Yace idan yana son kudi, waya kawai zai daga ya kira shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu kuma ya tabbatar kamin ya je gida kudin zasu shiga asusunsa.

Karanta Wannan  Najeriya ta zo ta daya cikin jerin kasashen Duniya da suka fi yawan coci masu girma

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *