
Babbar kotun tarayya dake Abuja ta bukaci hukumar zabe me zaman kanta data soke rijistar jam’iyyar ADC.
Kotun ta dauki wannan hukunci ne bayan da wasu ‘yan kishin kasa suka shigar da kara inda suke bukatar a soke rijistar jam’iyyun siyasa 5 ciki hadda ADC ,sauran sune Action Peoples Party (APP), Action Alliance (AA), Accord Party (AP), da Zenith Labour Party (ZLP).
Masu shigar da kara sun bayyana cewa, jam’iyyun sun kasa cika sharudan da ake bukata na kasancewar jam’iyyar siyasa,.
Sharudan sune kowace jam’iyya akalla ta yi nasarar kaso 25 a zaben shugaban kasa daga kowace jiha, ko kuma ya zamana tana da zababben dan siyasa a matakin kasa, Jiha ko karamar hukuma.
Saidai suka wadancan jam’iyyun basu cika wadannan sharudan ba.
Masu shigar da karar sun bukaci cewa, kotu ta tabbatar INEC ta soke rijistar wadannan jam’iyyun kamin zaben 2027 sannan ta hana jam’iyyun gudanar da duk wata harka ta siyasa da shiga zabe sannan a hana INEC mu’amala da wadannan jam’iyyun.
Idan dai wannan fata ya tabbata, ‘yan takarar wadannan jam’iyyun irin su Atiku Abubakar ka iya samun tankarda.