
Zuwan taurarin fina-finan Hausa wajan bikin ranar Dimokradiyya ta kasa Abuja ya bar baya da kura.
Da yawa sun rika sukar ‘yan fim din da fadin cewa bai kamata ba abinda suka yi musamman yayin da takwarorinsu na kudu ke zanga-zanga da nuna damuwa kan harkar matsalar tsaron Najeriya.
Dan Tiktok, Gfresh Al-amin ya bayyana cewa, abinda aka baiwa ‘yan fim din bai wuce Naira 150,000 ba kowanne wanda yace ba kudin yanke talauci bane.
Yace idan basu fito suka yi zanga-zanga ba, bai kamata a gansu suna murna ba.