Saturday, June 27
Shadow

Likitoci 550,000 ne suka rage a Najeriya, gida 16,000 sun tsere zuwa kasashen Turawa

Wata kungiyar Likitocin Najeriya ta koka da yawan tserewar Likitoci daga Najeriya zuwa kasashen Turawa.

Kungiyar tace a yanzu Likitoci 55,000 ne suka rage a Najeriya. Wanda sune ke kula da ‘yan Najeriya mutane Miliyan 220.

Likitocin sun bayyana hakane a wata ganawa da suka yi a Asibitin masu fama da rashin lafiyar kwakwalwa dake Yaba Lagos.

Shugaban kungiyar Likitocin, Prof Omoti Ernest ya bayyana cewa, sun yiwa Likitoci 130,000 Rijista amma zuwa yanzu guda 55,000 ne kadai ke aiki a Najeriya.

Hakan na nufin duk likita daya yana duba marasa lafiya tsakanin 3,600 zuwa 4000.

Sun yi kiran a dauki matakin hana likitoci tserewa daga Najeriya dan gujewa tabarbarewar harkar Lafiya a kasar.

Karanta Wannan  Ku yi hattara da abinda kuke dorawa a kafafen sadarwa, yanzu Haka Gwamnati ta kulle shafuka Miliyan 13 da suka dora abubuwan da basu dacw ba a Soshiyal Midiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *