
Baba Dan Audu, Watau Rabiu Rikadawa ya sanar da ficewa daga tafiyar Dauda Kahutu Rarara.
Saidai bayan ficewarsa, daya daga cikin yaran Rarara, Usman A. Adam ya bayyana cewa, Rashin gaskiyar da yake yi ne a film yaso yi musu shiyasa aka samu matsala dashi.

Kuma Usman ya rika kiran Baba Dan Audu da Barawo.
A wata hira da DCLHausa ta yi dashi, Rikadawa yace Naira Miliyan 200 gwamnatin jihar Gombe ta basu a ziyarar da suka kai.
Saidai ba Rikadawa ne kadai ya fice daga tafiyar Rarara ba akwai irinsu Mansurah Isah da Fati KK.