
Rahotanni daga birnin Bueno Aires na kasar Argentina ya bayyana cewa, mutanen kasar sun tayar da tashin hankali bayan nasarar Spain akan ‘yan kwallon kasarsu.
Spain ta dauki kofin Duniya bayan cin Argentina da kwallo daya me ban haushi.
A Bidiyon dake yawo a kafafen sadarwa, an ga ‘yan kasar Argentina nata jifar ‘yansanda duwatsu.
Yayin da su kuma ‘yansandan ke ta watsawa masu zanga-zangar hayaki me sa hawaye da kuma ruwan zafi.