Wednesday, September 9
Shadow

Matar mutuminnan dake zargin Sheikh Dr. Ahmad Gumi da rike masa mata ta yi magana

Khadija Diab, ‘yar kasar Morocco da mijinta ke zargin Sheikh Dr. Ahmad Gumi da riketa na tsawon watanni 11 ta yi magana a karin farko.

Khadija tace da farko dai Mijinta Nasiru Idris Makaryacine, ya mata karyar yana da wadata, kuma yana da aiki.

Tace tun kamin su zo Najeriya ya mata alkawarin cewa ba zata zauna gida daya da matarsa ba ya tanadar mata gida.

Amma da suka zo ita da magaifiyarta, sai ya ajiyesu a otal sannan ya rika rokonta wai ta yadda ta zauna gida daya da matarsa amma ta kiya

Tace da yaga ba zata hakura ba shine ya kama mata gida amma bai saka komai ba a ciki, data masa magana yace a hankali zai rika sayo kayan gidan.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Sabuwar Wakar da Rarara yayi ta Malam yayi Rawa wadda ake cewa da Pantamin yake

Tace ta mai magana ya sai mata injin wanki amma yaki, tace dole da hannu ta rika wanki wanda bata saba da hakan a kasarsu ba.

Tace da kanshi ya kaita wajan Sheikh Gumi ita da mahaifiyarta yace malaminsa ne kuma kamar uba yake a wajansa yana girmamashi.

Tace da mahaifiyarta ta tashi komawa kasar Morocco, sai ta samu Sheikh Gumi tace masa ga amanar ‘yarta nan ya zamar mata uwa da uba idan tana da wani damuwa ta je ta gaya masa.

Tace abubuwa suka ci gaba da munana a zamanta da Nasiru ba abinci, baya kaita Asibiti in bata da lafiya saidai ya kaita Kemis.

Karanta Wannan  Coci a jihar Delta ta kori Reverend Fr. Daniel Okanatotor saboda ya je kasar Amurka yayi aure a boye wanda a dokar kiristanci bashi ba aure tunda ya kai mukamin Priest

Tace akwai lokacin da Sheikh Gumi ya rika musu sulhu, sannan akwai sanda ma har kudi ya basu yace su sayi abubuwan da basu dashi a gida.

Tace Sheikh Gumi ya taba zuwa gidansu dan ya ganewa idansa korafin da take cewa bata da komai na biyan bukata a gida.

Tace da yace ya cema mijinta ya sai mata kayan biyan bukata shine yake cewa ba zai siya ba kuma babu ubanda ya isa ya sashi yayi abinda bai yi niyya ba.

Yace saidai in sakinta zai yi, tace ita kuma daga nan ne tace ba zata ci gaba da zama dashi ba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon abin ban mamaki: Wata tsohuwar malamar Jinya(NURSE) tace sukan canjawa mata jarirai bayan sun haihu, wani lokacin ma sukan dauke Jariri su ajiye ma me jego Mattaccen Jariri, su sayar da natan

Tace ta koma gidan Sheikh Gumi da zama kuma itace tace ba zata koma gidan mijin nata ba.

Tace ta kaishi Kotu amma akaita daga shari’a saboda baya zuwa zaman kotun tace kuma sai kokarin canja maganar yake.

Tace yanzu tana kasarsu Morocco kuma tana baiwa Sheikh Gumi Hakuri kan irin tsaka mai wuya data sakashi.

Tace a fadan da suka yi na karshe da Mijinta, ya kaita kofar gidan Sheikh Gumi, ko jira bai yi ba an bude mata kofa ya juya ya tafi ya barta a tsaye.

Tace daga nan ne tace ba zata koma gidansa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *