
Jigo a jam’iyyar Labour Party, Mr. Abayomi Arabambi ya shigar da kara a gaban kotu inda yake neman WAEC da jami’ar UNN, da Hukumar bautar kasa ta NYSC su bayyana ainahin takardun karatun dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi
Yace ya aikawa Hukumomin da bukatar hakan amma sun ki, dan haka yake neman kotu ta tursasasu.
Bayanshi, akwai kuma mutane 2 da suma suka shigar da kara akan neman takardun ainahi na karatun Peter Obi wanda jimullarsu ya kai 3 kenan.
Arabambi yace bawai yana zargin takardun bogine Peter Obi ke amfani dasu ba, yana son wadannan hukumomi su bayyanawa Duniya ainahin takardun karatun na peter Obine.