Thursday, September 17
Shadow

Zee Gombe ta fitar da sanarwa kan sautun murya na wayar da suka yi da Malam Isa Ali Pantami dake yawo

Tauraruwar Tiktok ta Jihar Gombe, Zee Gombe ta fitar da bayanai kan Sautin murya na waya dake yawo a kafafen sadarwa wanda suka yi ita da Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami.

Zee Gombe tace ba itace ta fitar da sautin muryar ba sannan kuma an yi Amfani da AI wajan gyara sautin Muryar.

Ga bayaninta kamar haka:

Ina ganin ya zama dole in fito fili in yi wannan bayani domin in fayyace abin da ke faruwa game da wani sautin tattaunawa da ake yadawa a kafafen sada zumunta.

Da farko, ina so jama’a su fahimci abu guda: ba ni ce na fitar da wannan sautin ba.

Amma abin da ya fi damuna yanzu shi ne yadda ake yada wasu abubuwa da ake danganta su da wannan tattaunawar, alhali ba su ne ainihin abin da aka tattauna ba.

Karanta Wannan  Wani ɗan asalin jihar kano, mazaunin Faransa ya kafa sabon tarihi a fannin kimiyya

Akwai wani sauti da ake yadawa wanda aka yi masa gyara ko kuma aka ƙirƙira shi ta hanyar AI, kuma abin da ake ji a cikinsa ba ya wakiltar ainihin tattaunawar da aka yi. Wasu daga cikin kalmomin da ake ji a cikin wannan sigar ba su ne abin da aka faɗa a tattaunawar ba.

Saboda haka, ina roƙon jama’a: don Allah ku daina yaɗa duk wani sauti ko bidiyo kawai saboda kun gan shi a social media. Ba duk abin da ake yadawa ba ne gaskiya.

Wannan magana ta fara shafar mutane da dama, har da ni da Malam Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami. Wasu suna amfani da wannan abin da ake yadawa wajen yi mana baƙar magana da ƙirƙirar labarai waɗanda ba su dace da abin da ya faru ba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Yanda wani dan kasar Ghana ya hadu da shugaban kasar UAE suka gaisa yayin da shugaban ke ran gadi

Ina so in bayyana a fili cewa ban taɓa da niyyar fitar da wata tattaunawa ta sirri domin a yaɗa ta a bainar jama’a ba. Kuma ban amince da duk wani sauyi, gyara ko ƙirƙirar magana da aka yi wa wannan sauti ba.

Idan mutum yana son sanin gaskiya, ya kamata ya nemi ainihin bayani, ba ya ɗauki abin da aka tura masa a WhatsApp ko social media ya ɗauka cewa shi ne gaskiya.

Ni na san abin da aka tattauna, kuma na san abin da ban faɗa ba. Saboda haka, ba zan yarda a ɗora min kalaman da ban faɗa ba, ko kuma a yi amfani da wani sautin da aka gyara wajen bata min suna ko bata wa wani suna.

Karanta Wannan  Ba a cire Atiku a matsayin Wazirin Adamawa ba — Gwamnatin Adamawa

Don Allah ku daina yaɗa abin da ba ku tabbatar da gaskiyarsa ba.

Wannan ba batun siyasa kawai ba ne. Batun gaskiya ne, mutunci ne, da kuma kare sunan mutane daga abubuwan da ba su faru ba.

Ina roƙon kowa ya yi hankali da abin da yake yadawa. Ba duk abin da kuke ji ko gani a social media ne gaskiya ba.

Gaskiya za ta fito insha allah🥲👏

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *