
Wani magidanci daga Arewacin Najeriya ya tare wata mota ta hanyar shiga gaban motar inda ya bayyana cewa, matarsa ce a cikin motar tare da kwartonta.
Jama’a sun taru inda daga baya jami’an tsaro suka isa wajan.
An ga Mijin matar da wanda yake zargi da neman matarsa suna musayar zage-zage.
Bidiyon lamarin ya karade kafafen sada zumunta inda akai ta tafka Muhawara.