
Allah sarki, Wannan wani sojan Najeriya ne da yake rokon Allah ya dauki Rayuwarsa saboda ya gaji da rayuwa.
Yace yasan Rokon Mutuwa babu kyau.
Amma yace Allah shidai kawai so yake ya bar Duniyarnan, saboda kalubalen da yake fuskanta ya masa yawa.
Yace da bai da iyaye, da Mata Wallahi da ajiye aikin sojan zai yi ya koma gida ya rika zuwa Masallaci yana salati.