
Wannan wata matashiyace da wani da bata sani ba ya dauketa zuwa Otal.
Kamin su kama daki, Sun zauna a Reception yace me za’a kawo mata tace ruwa.
Saidai yace a kawo mata yogot.
Suna zaune ya fara waya, ya nuna irin ba’a jinsa dinnan.
Sai yace ta bashi wayarta ya kira, wanine yakewa kwatance zai zo ya samesu a otal din.
Ya karbi wayarta ya nuna alamar ya kira waya, ya fita waje yana fadar ga inda zaka bi kazo.
A haka ya bace, ya barta, bai biya kudin ruwan da ya sha da yogot din da aka kawo mata ba, gashi ya tsere da wayarta.