
Bidiyon yanda ake rike da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu hagu da dama lokacin da yake tafiya a jihar Rivers ya dauki hankula.
An ga jami’an tsaronsa rike da hannunsa kuma suna daf dashi suna tafiya tare.
Har an ga dan shugaban kasar, Seyi Tinubu shima a gaba yana juyawa yana kallon mahaifin nasa.