Friday, December 5
Shadow

An samu banbancin ra’ayi: Yayin da Kwankwaso yace masu zàngà-zàngà su bari sai lokacin zabe su canja wanda basu so, Abba Gida-Gida yace yana goyon bayan zàngà-zàngàr kuma ma zai iya shiga a yi dashi

{“remix_data”:[],”source_tags”:[],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Gwamnatin jihar Kano, a karkashin gwamna Abba Kabir Yusuf ta sanar da goyon bayan masu zanga-zangar kan tsadar rayuwa.

Gwamnan da kansa ne ya bayyana hakan a wajan wani taro na masu ruwa da tsaki da aka gudanar ranar Laraba a Kano.

Gwamnan yace muddin za’a yi zàngà-zàngàr cikin tsari ba tashin hankali zai karbi masu zanga-zangar a fadar gwamnati.

Yace idam suna so ma zai shiga shima a yi dashi.

Gwamnan yace kundin tsarin Mulkin Najeriya ya bayar da damar yin zanga-zangar.

Saidai wannan ra’ayi nasa ya sha banban dana tsohon gwamnan jihar wanda ake ganin me gidansa ne watau Dr. Rabiu Musa Kwankwaso.

Karanta Wannan  ALLAHU AKBÀR: Yau Marigayi Shéikh Abubakar Gero Argungu Ke Cika Shekara Guda Cif Da Rasuwa

A baya dai mun samu rahoton cewa, Kwankwaso ya bayar da shawarar a hakura da yin zanga-zangar a bari sai idan lokacin zabe yayi a fito a zabi wanda ake so.

A wani rahoton me kama da wannan kuma mun samu cewa, Wani rahoton sirri daya bayyana yace Kwankwaso na daya daga cikin manyan mutanen da aka baiwa kwangilar hana zanga-zangar musamman a jihar Kano, ganin cewa yana daya daga cikin masu fada aji na jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *