Monday, December 16
Shadow

Tsawon gashi cikin sati daya

Ana iya samun tsawon gashi cikin sati daya idan aka yi abinda ya dace kamar yanda zamu yi bayani a kasa:

Hanya ta farko da ake iya kara gashi cikin sati daya itace ta amfani da man kwakwa, ko man Zaitun.

Yanda ake yi shine, ana samun man kwakwa ko kan zaitun a dafashi, a sauke ya huce,amma kada a bari ya huce gaba daya, sai a taba da hannu a ji idan akwai dumi yayi daidai yanza za’a iya shafawa akai sai a rika dangwala ana shafawa akai, a shafa sosai ya shiga cikin gashi da kyau.

A tabbatar an gauraye duka gashin dashi. A bari yayi mintuna akalla 30 sannan a wanke da shampoo.

Karanta Wannan  Gyaran gashi da wiwi

Hakanan masana sun kara da cewa, cin abinci me gina jiki da kyau da kuma motsa jiki da kuma murza gashin kai akai-akai watau a rika yi mai tausa har zuwa inda ya tsiro yana taimakawa kara yawan gashi sosai.

Hakanan masana sun ce zafin Hair Dryer da sauran injinan da ake amfani dasu wajan gyara gashi masu buso zafi yanawa gashi illa, yana da kyau a rage zafin kamin a rika busar da gashin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *