Monday, December 16
Shadow

Kuma Dai:EFCC ta sake kama wani matashi saboda lika Kudin Naira a wajan biki a jihar Gombe

Hukumar yaki da rashawa da cin hanci ta EFCC ta sake kama wani matashi a jihar Gombe me suna Zachariyya Muhammad saboda yin likin kudin Naira a wajan wani biki.

An kama shine ranar Asabar, 24 ga watan Mayu bayan ya lika kudin Naira dari 200 a wajan wani bikin G-Connect.

Ko da aka nuna masa bidiyonsa yana likin, ya amsa cewa lallai shine, hukumar zata gurfanar dashi a gaban kotu.

A baya dai EFCC ta kama mutane da yawa a jihar Gombe shima.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *